✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta rufe asusun Gwamnatin Kogi kan karkatar da albashi

Ana zargin gwamantin jihar da karkatar da N20bn na albashi da ta karba rance.

Kotu ta rufe asubun bankin Gwamnatin Jihar Kogi kan zargin karkatar kudin albashin ma’aikata Naira biliyan 20.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Legas ta rufe Asusun Tallafin Albashin Gwamnatin Jihar Kogi mai lamba 0073572696 a bankin Sterling har sai an kammala bincike kan zargin karkatar da kudaden.

Hukumar yaki da cin hanci (EFCC) ta maka Gwamnatin Jihar Kogi a kotun ne bisa zargin karbar Naira bililyan 20 rance domin biyan albashi ma’aikata daga bankin Sterlin, amma ta karkatar da kudaden domin samun kudin a kansu.

A don haka hukumar ta mai neman kotun ta hana gwamantin jihar taba kudaden da ke cikin asusun.

Lauyan EFCC, A. O. Mohammed, ya shaida wa kotun cewa Gwamnatin Jihar Kogi ta karkatar Naira biliyan 20 da Bankin Sterling ya ba ta rance domin biyan bashin albashin ma’aikata, zuwa wani asusunta a bankin na Sterling domin samun riba.

A cewarsa, maimakon amfani da kudaden wajen abin da ya sa aka ta rancen, Gwamantin Jihar Kogi umarci bankin Sterling ya tura kudin daga asusun rancen zuwa wani asusunta na daban da take ajiya na tsayayyen lokaci a bankin.

Lauyan ya kara da cewa zuwa yanzu, bankin ya kasa ba wa hukumar  wata kwakkwatar shaida da za ta nuna cewa kudaden ba sa fuskantar wata barazana.

Da yake amincewa da bukatar ta EFCC, alkalin kotun, Mai Shari’a Tijani Ringim ya umarci hukumar ta wallafa umarnin kotun a babbar jarida guda daya, sannan ta rika fitar da rahoho duk bayan wata uku kan inda aka kwana a binciken.

Daga nan alkalin ya dage zaman zuwa ranar 1 ga Disamba, 2021, ranar da za a gabatar da rahoton binciken na EFCC.