✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta mallaka kudi da gidaje 6 na kamfanin marigayi Badeh ga gwamnati

Wata kotu a Abuja a ranar Litinin da ta gabata ta kwace wasu manyan gine-gine shida da tsabar kudi Dala miliyan daya daga wani kamfani…

Wata kotu a Abuja a ranar Litinin da ta gabata ta kwace wasu manyan gine-gine shida da tsabar kudi Dala miliyan daya daga wani kamfani da aka gano cewa mallakin marigayi tsohon Babban Hafsan Tsaro ne, Iya Mashal Aled Badeh ta mika Wa Gwamnatin Tarayya su.

Mai Shari’a Okon Abang na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin cewa a kwace kamfanin Iyalkam Nigeria Ltd, wanda aka gano  mallakin marigayi Badeh ne kuma a can baya ya shiga yarjejeniya da Hukumar Yaki da Almundahana (EFCC) dangane da amsa wasu laifuffuka da suka danganci kudi da aka tuhumi kamfanin da aikatawa.

Bisa dogaro da wannan yarjejeniya ta amsa aikata laifi da kamfanin ya yi, ya sa Mai shari’a Abang ya hukunta shi kan laifuffuka 10, kamar yadda Hukumar EFCC ta gabatar wa kotun. Sai dai kuma an tsame sunan Badeh daga shari’ar, kamar yadda aka yi gyara a takardar tuhumar.

Mai shari’ar ya ce: “Kamar yadda aka yi la’akari da yarjejeniyar amsa laifi da aka yi maslaha a tsakanin bangarorin biyu, an rushe kamfanin Iyalkam Nigeria Limited kuma za a aika wa Hukumar Yi wa Kamfanoni Rajista (CAC) bayanin hukuncin domin ta dauki matakin da ya dace da shi.”

Gine-ginen da hukuncin kotun ya shafa sun hada da wani babban gida mai lamba 6 a Ogun Riber Cresecent, Maitama Abuja mai kimar Naira biliyan 1.1. Sai ginin da ke dauke da rukunin shaguna da ke Lamba 1386, Oda Crescent, Cadastral Zone A, Unguwar Wuse II Abuja, mai kimar Naira biliyan 1.6. Akwai tagwayen gidaje a Unguwar Wuse II, na ‘ya’yan marigayi Aled Badeh masu kimar Naira miliyan 260, daya Naira miliyan 330.

Haka akwai wani gidan da ke Lamba 2, Nelson Mandela Street, Asokoro Abuja, wanda aka yi wa kwaskwarima a kan Naira miliyan 62. Akwai kuma gidan marigayi Badeh da ke garin Yola Jihar Adamawa, wanda aka gina shi a kan Naira miliyan 150.

Bayan ga wadannan gine-gine, akwai kuma tsabar kudi da suka kai Dalar Amurka miliyan daya, wadanda aka samu a gida mai Lamba 6, Ogun Riber Crescent, Unguwar Maitama Abuja a watan Fabrairun shekarar 2016.

Tunda farko dai an fara gurfanar da marigayi Badeh ne a gaban kotu, ana tuhumarsa da aikata laifuffuka 14, inda aka yi wa tuhumar kwaskwarima. An tuhume shi ne da aikata laifuffukan cin amana, almundahana a yayin aikin gwamnati da kuma sace kudi da suka kai Naira biliyan 3.9.

A lokacin da aka tado maganar shari’ar a kotu a watan Janairun da ya gabata, Lauyan Badeh, Akin Olujimi (SAN) ya shaida wa kotu cewa Badeh ya mutu, inda ya bukaci a dage shari’ar domin ya samu damar ganawa da lauya mai shigar da kara, Leke Atolagbe.

Bayan kotu ta dawo don ci gaba da shari’ar a ranar Litinin da ta gabata, Atolagbe ya bayyana wa kotun batun yarjejeniya da maslaha da suka cimmawa da kamfanin, inda kuma suka yi wa tuhumar kwaskwarima ta dawo guda 10 maimakon 14.