✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta kwace gidaje da filaye 24 na Abdulrasheed Maina

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin kwace kadarori 23 da ake kyautata zaton na tsohon shugaban gyara harkar fansho (PRTT), Abdulrasheed Maina,…

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin kwace kadarori 23 da ake kyautata zaton na tsohon shugaban gyara harkar fansho (PRTT), Abdulrasheed Maina, ne.

Wadannan kadarorin  sun hada da: filaye da gidaje, za a mallakawa gwamnatin tarayya su Alkaliyar kotun Folashade Giwa Ogunbanjo, ce ta bada umurnin a yau Talata, yayin da take yanke hukunci kan karar da Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta shigar.

Hukumar EFCC ta bukaci kotun ta sadaukarwa gwamnati dukiyoyin da ke da alaka da Abdulrashid Maina.

Kotun ta bukaci izinin gwamnati ta wallafa dukkan dukiyoyin a jaridu saboda duk wanda ke da hujjar cewa, dukiyarsa ya fito ya kawo hujja.  Wadannan dukiyoyin da aka sadaukar na jihohin Kaduna, Borno, Sakkwato da Abuja.