Kotun sauraren kararrakin zaben Shugaban Kasa, ta bayyana cewa ba ta da hurumin sauraren karar da jam’iyyar APM ta shigar tana kalubalantar cancantar takarar shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima.
Da yake karanta hukuncin a ranar Laraba, Mai Shari’a Haruna Tsammani, ya ce batutuwan da aka gabatar a gaban kotun su ne batutuwan da suka shafi gabanin zabe, wadanda ya kamata a ce sun kasance a wata babbar kotu.
- Kotu ta soke zaben Sanatan APC a Kogi, ta ce ’yar takarar PDP ce ta lashe
- Muhimman ayyuka 10 da Abba ya yi a kwana 100 a Kano
Ya kara da cewa wa’adin kwanaki 180 da za a tantance lamarin ya wuce.
“Kotun zabe ba ta da hurumin zaben fidda gwani na jam’iyyar siyasa,” in ji shi.
Ya ce abubuwan da suka shafi cancanta da rashin cancantar suna sashe na 131 da 137(1)(a)(j) na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Ya ce batun da ake korafin ya shafi jam’iyyar siyasa.
APM ta yi ikirarin cewa Tinubu da Shettima ba a tantance su ba a ranar 25 ga watan Fabrairu ba.
Sun kara da cewa kwanakin da ware na maye gurbin Kabiru Masari da Kashim Shettima bai yi daidai da sashe na 33 na dokar zaben 2022 wanda ya tanadi kwana 14 na maye gurbin dan takarar.