✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta kori dan takarar Gwamnan Kano na PDP

Babbar kotun da ke Jihar Kano ta kori dan takarar Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar adawa ta PDP, daga cikin sauran ‘yan…

Babbar kotun da ke Jihar Kano ta kori dan takarar Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar adawa ta PDP, daga cikin sauran ‘yan takarar Gwamnan da za a yi ranar Asabar mai zuwa.

Kabir shi ne dan takarar da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya tsayar a matsayin dan takarar Gwamnan jihar na jam’iyyar PDP.

Mai shari’a na kotun Lowis Allagoa ya bukaci jam’iyyar da ta gudanar zaben fidda gwani daga yau zuwa ranar 9 ga Maris 2019.