✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarautar Kano: Kotu ta yi watsi da bukatar neman tsige Sarki Sanusi II

Kotun ta ba da umarnin biyan Aminu Ado Bayero diyyar Naira miliyan 10

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta ba da umarnin biyan tatar ga Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero kan umarnin da gwamnatin jihar ta bayar na tsare shi da kuma fitar da shi daga Fadar Nassarawa.

Kotun ta kuma yi watsi da bukatar Aminu Ado Bayero ta neman fitar da Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II daga Fadar Gidan Rumfar.

Lauyan Sanusi, Ibrahim Isa Wangida, ya bayyana hukuncin a matsayin nasara, kasancewar bai soke dokar masarautun jihar Kano da ta nada wand yake karewa ba.

Duk da haka ya ce zai tattauna da Sanusi II gamr da ko za su daukaka kara kan tarar miliyan 19 da kotun ta sanya.

Mai Shari’a Simon Amobeda ya yanke wannan hukunci ne kan karar da Sarki Aminu ya shigar na neman karw hakkinsa ba dan Adam da kuma na walwala ba tare da kaidi ba a Jihar Kano.

A nasa bangaren lauyan Aminu Ado Bayero, Abdulrazaq Ahmad, ya ce hukuncin ya hana gwamnatin jihar da hukumomin tsaro fitar da wanda yake karewa daga Fadar Nassarawa ko kuma tsare shi.

Ya kara da cewa hukuncin ya kara tabbatar da matsayinsu na cewa kotun tana da hurumin sauraren karar neman hakkin wanda yake karewa da ake neman takewa.