✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ki sauraron karar da Binani ta shigar da INEC kan zaben Adamawa

Ta shigar da karar ce tana son kada INEC ta sake bayyana sakamakon

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ki sauraron karar da ’yar takarar APC, Aisha Dahiru Binani ta shigar tana neman a hana INEC sanar da sakamakon zaben Gwamnan Jihar Adamawa.

Lokacin da aka karanta bukatar a gaban kotun ranar Talata, alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya bukaci lauyoyin Binani da su yi wa kotun bayani kan huruminta a kan batun cikin kwana uku.

Kazalika, alkalin ya kuma ki amincewa da bukatar lauyan jam’iyyar PDP da Gwamna Ahmad Fintiri, Afeez Matomi, daga sake mika wata sabuwar bukata saboda kotun sauraron kararraki ce ke da hurumin sauraron hakan.

Sanata Binani dai ta ce matakin da INEC ta dauka na soke ayyanatan da aka yi a matsayin zababbiyar Gwamna ta yi gaban kanta ne wajen yin aikin kotu.

Sai dai kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Afrilu mai zuwa.