✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta ki amincewa da bukatar kwace kadarorin Saraki

Kotun ta yi fatali da bukatar kwace wasu kadarori mallakin tsohon Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Bukola Saraki.

Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Legas ta yi fatali da bukatar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC dake neman ta kwace wasu kadarori mallakin tsohon Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Bukola Saraki.

Kotun dai karkashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Liman a ranar Alhamis ta ki amincewa da bukatar ta EFCC kan kwace kadadrorin wadanda ke kan lamba 17A a kan titin McDonald dake Ikoyin jihar Legas.

A maimakon haka, kotun ta saurari shaidu na baki kafin daga bisani ta dage ci gaba da sauraron karar.

Dage shari’ar na zuwa ne bayan lauyan EFCC, Nnaemeka Omewa da lauyan Sarakin, Kehinde Ogunwumiju (SAN) sun gabatar da jawabansu na amincewa da kuma sukar bukatar dake nema a kwace kadarorin dugurungun.

Da take yanke hukunci, kotun ta ce amfanin bayar da umarnin kwace kadarorin na wucin gadi tun da farko shine don a hana wadanda ke tuhuma (EFCC) sun gamsar da kotun cewa wanda ake zargin ya same su ne ta haramtattun hanyoyi a karkashin dokokin yaki da cin hanci da rashawa na Najeriya.