✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta hana ’yan sanda da sojoji fitar da Sanusi daga fada

Kotun ta hana jami'an tsaron daga muzguna wa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta babbar kotun Kano da ke zamanta a kan titin Miller Road, ta hana ‘yan sanda da jami’an SSS da sojoji daga korar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga fada.

Sarkin ya shigar da karar ne tare da masu naɗin Sarkin Kano huɗu: Madakin Kano Yusuf Nabahani; Makaman Kano Ibrahim Sarki Abdullahi; Sarkin Bai Mansur Adnan da Sarkin Dawaki Maituta Bello Tuta.

Da ta ke tabbatar da umarnin, Mai shari’a Aliyu ta kuma ja kunnen jami’an tsaro daga kama ko muzguna wa Sarki Sanusi II.

Wannan dai na zuwa ne bayan dambaruwar rushe masarautun Jihar Kano, da majalisar dokokin jihar ta yi a makom da ya wuce.

Rushe masarautun tare da sarakunansu ya haifar da ruɗani da cece-kuce a jihar, inda wasu ke ganin matakin gwamnatin jihar ya saɓa wa doka.

A gefe guda kuwa, wasu magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero sun gudanar da zanga-zanga a ranar Lahadi a kan titin zuwa gidan gwamnatin jihar.

Zanga-zangar na zuwa ne bayan da tuɓaɓɓen Sarkin ya isa jihar a ranar Alhamis tare da sauka a ƙaramar fadar Nassarawa, tare neman a yi masa adalci kan tsige daga sarautar Kano.

Alƙalin ta ɗage ƙarar zuwa ranar 13 ga watan Yuni, 2024 don ci gaba da sauraron ƙarar.

Aminiya ta ruwaito cewa Mai shari’a Aliyu ta bayar da umarnin korar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga ƙaramar fadar Nassarawa a ranar Litinin.