✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure wata mata shekara biyu a kan damfara

Wata kotu ta daure wata mata mai suna Sa’adatu Isiyaku bayan ta same ta da laifin aikata damfarar Naira dubu 10 da nufin ba da…

Wata kotu ta daure wata mata mai suna Sa’adatu Isiyaku bayan ta same ta da laifin aikata damfarar Naira dubu 10 da nufin ba da tallafin kudi daga Gwamnatin Jihar Kaduna, inda kotun ta tura matar kurkuku na tsawon shekara biyu ko tarar Naira dubu 200.

Babbar Kotun Majistare da ke Zariya wadda Mai shari’a Umar Bature ke jagoranta ta zartar da hukunci bayan ta tabbatar da laifin da ’yan sanda suke tuhumarta da su a karkashin sashe na 307 na kundin dokokin Jihar Kaduna na shekarar 2017.

A shekaranjiya Laraba ce ofishin ’yan sanda da ke Dan Magaji a Zariya ya kama matar wacce ta tara mata tana karbar Naira dari bibbiyu daga hannunsu kan cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ce ta turo ta aikin tattara sunayen mata masu rauni domin tallafa musu da Naira dubu 10 kowace, domin yin sana’o’i.

Da Aminiya ta nemi jin ta bakin Sa’adatu Isiyaku bisa yadda aka yi, sai ta ce ita ba da son ranta ne ta aikata hakan ba, ta yi ne a kan babu, kuma mijinta ya rasu ya bar ta da da daya, kuma sannan ba wanda ya sa ta ta yi haka. “Don haka na yi nadamar abin da na aikata, kuma ina rokon gwamnati da jama’a a yi min afuwa,” inji ta.