Wata babbar Kotu a Jihar Gombe ta yanke wa wani magidanci da abokinsa hukunci daurin shekaru 17 a gidan yari saboda yin lalata da ’ya’yansa.
Kotun, karkashin Mai shari’a Joseph Ahmed Awak, ta samu mutanen biyu da laifin hada baki da aikata fyade ga kananan yara biyu mai shekara bakwai da mai shekaru tara, da aka sakaya sunayensu.
- Budurwar da ta jira saurayinta shekara 16 ya fito a gidan yari
- Budurwa da bindige saurayi don ya ki sumbatar ta
Kotun ta gano cewa tun a shekarar 2019 mahaifin yaran da abokin nasa suka kulla yarjejeniya, inda uban yake lalata da ’yarsa daya, yake kuma tura dayar zuwa gidan abokinsa yana lalata da ita a lokuta daban-daban, bayan sun yi wa yaran barazanar duka idan suka kuskura suka fadi abin da ke faruwa.
A cewar kotun, aikata hakan laifi ne a dokar kasa sashe na 97 da sashi na 282 na kundin laifuka da hukunci Penel Code, sai dai mutanen sun musanta laifin da ake zargin su da aikatawa.
Hakan ne ya sa mai gabatar kara kuma lauyar Gwamnatin Jihar Gombe, Barista Hafsat Aliyu Abubakar, ta gabatar da shaidu mutum shida kuma suka tabbatar da faruwar lamarin.
Bayan shi ma ya yi wa shaidun tambayoyi, lauyyan wadanda ake tuhuma, Barista Yakubu Chidima, ya gabatar da nashi shaidun na mutum biyu, wadanda kanne ne ga wadanda ake zargi.
Daga bisani ita ma lauyar gwamnatin ta yi musu wasu tambayoyi, sai dai daga karshe wadanda ake zargi sun gaza kare kansu.
Daga nan ne sai alkalin kotun, Mai Shari’a Joseph Ahmed Awak, ya yanke wa mahaifain yaran hukuncin zaman gidan kaso na shekara 17, abokin nasa kuma hukuncin daurin shekara 10.