Alkalin wata kotun majistare da ke Ikeja a jihar Legas, Oluwatoyin Taiwo, ta yanke wa Moses Joseph hukuncin shekara 37a gidan kaso bisa samunsa da laifin yi wa wata karamar yarinya fyade.
Kafin yanke hukuncin dai lauyan wanda ake tuhuma ya roki kotun ta sassauta wa Moses, saboda mutuwa da dan uwansa ya yi bayan samun labarin kama shi, kuma wannan ne karo na farko da ya aikata laifin.
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 10 a hanyar Jos zuwa Bauchi
- Na yi mamaki da na ji an ce Salman Rushdie bai mutu ba – Wanda ya caka masa wuka
Lauyan ya kuma ce baya ga haka, shi n yake kula da gidansu, ga kuma gudun zubewar mutuncinsa a idon mahaifiyarsa wacce tsohuwa ce.
An dai kama Moses ne tun a watan Satumban 2021, bisa zarginsa da yi wa karamar yarinyar fyade.
Alkali Oluwatoyin Taiwo ta ce ta gamsu da hujjojin da aka gabatar mata kan wanda ake zargin.
“Sakamakon samun wanda ake tuhuma da lafin farko na fyade, an yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai, sai laifi na biyu na cin zarafin karamar yarinya, daurin shekarula 30, kuma zai yi su ne a jere,” inji alkalin.
Laifin dai ta ce ya saba wa sashe na 137 na kundin manyan laifukan jihar Legas na shekarar 2015.