✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure miji saboda kara aure ba tare da izinin matarsa ba

Kotun ta daure mijin sakamakon kara aure ba tare da izinin matarsa ba.

Wata kotu a kasar Pakistan ta daure wani mutum wata shida a gidan yari saboda ya kara aure ba tare da amincewar matarsa ba.

Kotun da ke Lahore ta yi watsi da ikirarin mutumin mai suna Shahzad Saqib da ya ce addininsa ya ba shi damar kara aure a matsayinsa na musulmi.

Matar ta shi Ayesha Bibi, ta yi nasara a kotun, bayan ta yi ikirarin cewa karin auren ba tare da amincewarta ba, ya saba wa dokar iyali ta kasar Pakistan, lamarin da ya sa kotun ta ci kuma tarar mijin dala dubu biyu.

Masu fafutikar kare hakkin mata, sun ce hukuncin zai karya guiwar mazan da ke da niyyar karin aure ko cin amanar matansu, kuma zai bude wa mata kofar neman hakkinsu a kotu.

A kasar Pakistan maza na auren mace fiye da daya, amma dole sai namiji ya nemi amincewar matarsa ta farko kafin ya samu damar kara ta biyu.

Yanzu Saqib na da damar daukaka kara kan hukuncin kotun da ta yanke masa.

An dade Majalisar harkokin addinin Islama da ke kasar Pakistan, na kalubalantar dokar iyali ta kasar tare da ba gwamnati shawarwari da suka shafi harakokin addini.