Wata kotu da ke zamanta a Ado-Ekiti, Jihar Ekiti, ta daure wani manomi mai shekara 29 a gidan kaso bisa samun shi da laifin aikata fyade.
Da take bayyana wa kotu yadda lamarin ya faru, yarinyar mai shekara 17 ta ce: “Na je gonar kakata ne don na tsinko mana tattasai, sai wannan manomin ya zo ya ce na ba shi ruwa da kwakwar manja, sai na ce masa ba ni da ruwa, kuma gonar ba tawa ba ce ta kakata ce”.
- Gwamna Bala ya sake nada tsohon dan takarar gwamna mukamin Sakataren Gwamnati
- Sarauniyar Ingila Elizabeth II ta cika shekara 70 a kan mulki
“Sai ya tafi, ba a jima ba sai ga shi ya dawo da tsumma, ya cakume ni ya daure min baki, ina ta ihu amma ya fi ni karfi shi ne ya ci zarafina.
“Har da yi min duka da karan rogo saboda wai acewarsa na bata masa lokaci, ina kuka na tafi gida, mutanen da na gamu da su a hanya ne suka kai ni asibiti, sannan suka sanar da iyeyena”, in ji ta.
Bayan shaidu biyar da lauyan mai kara ya gabatar ga kotun, akwai bayanin asibiti, an gabatar da kayan jikinta lokacin da abin ya faru a matsayin shaida.
A nasa bangaren, wanda ake tuhumar ta bakin lauyansa, Gbenga Abiola, ya ce ba shi da wata shaida.
A nan ne Mai Shari’a Adeniyi Familoni ya yanke hukunci, in da ya ce mai kara ta gabatar da gamsassun hujjoji don haka kotu ta daure wanda ake zargin tsawon shekaru 10.