✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure magidanci  rai-da-rai saboda yin lalata da jikarsa

Wata Babbar Kotu da ke Ringim a Jihar Jigawa a karkashin Mai shari’a Ahmed Abubakar Kazaure ta daure wani magidanci mai suna Nafi’u mai shekara…

Wata Babbar Kotu da ke Ringim a Jihar Jigawa a karkashin Mai shari’a Ahmed Abubakar Kazaure ta daure wani magidanci mai suna Nafi’u mai shekara 39 mazaunin kauyen Dan Kyada da ke kasar Dagacin Muku a Karamar Hukumar Garki, rai-da-rai bayan samunsa da lalata da jikarsa.

Kotun ta daure tsohon rai-da-rai ne saboda samunsa da laifin yi wa jikarsa ’yar shekara 9 fyade.

Rahotannin sun ce lamarin ya faru ne bayan mutanen gidan sun tafi unguwa sai ya shiga ban-daki da niyyar wanka sai ya kira jikar ta kawo masa soso da sabulu, inda ya kama ta ya yi mata fyade.

Mai shari’a Ahmed Kazaure ya ce kotu ta yanke wa wanda ake tuhumar hukuncin ne sakamakon kwararan shaidu, kuma bai musanta laifinsa ba.