Wata kotu a Jihar Georgia da ke Amurka, ta yanke wa wani Fasto zaman gidan yari na shekara 10 bisa laifin yi wa wata yarinya ’yar Uganda mai shekara 14 fyade.
Faston ya aikata laifin ne a lokacin da yarinyar ke karkashin kulawarsa a majami’ar Orthodox Presbyterian da ke yankin gabashin Mbale a Uganda.
Bayan zaman gidan sarka da Eric Tuininga mai shekara 45 wanda fito daga garin Milledgeville da ke jihar Georgia zai yi a kurkukun Amurka, zai kuma biya tarar dala dubu 20 da za a bai wa yarinyar.
Sannan zai shafe duka rayuwarsa bayan sakin sa daga kurkuku a matsayin wanda hukuma take lura da shi da yi masa lakabi a matsayin wanda ya taba gudanar da cin zarafin jinsi.
BBC ya ruwaito cewa, dan mishan din wanda ya yi zaman wakafi yayin da ake shari’ar, ya amsa laifinsa a watan Fabrairun wannan shekara.
Kamar yadda wata sanarwar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta nuna, wani Ba’amurke ne mai alaka da majami’ar Orthodox Presbyterian da ke zaune a Mbale ya tuntubi Ofishin Jakadancin Amurka a watan Yunin 2019 domin kai karar Tuininga.
Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta binciki zargin, tare da taimakon Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurkar da Ofishin Tsaro na Diflomasiyya (DSS) da ke birnin Kamfala a Uganda.