✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta daure Abdulrasheed Maina shekara 61 kan badakalar fansho

Kotun Tarayya ta kama shi da laifin satar sama da Naira biliyan 2 na ’yan fansho.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke hukuncinn daurin shekara 61 a kan tsohon Shugaban Hukumar Kula da Gyaran Fansho ta Kasa (PRTT), Abdulrasheed Maina.

Kotun ta yanke hukuncin ne a zamanta na ranar Litinin bayan ta kama Maina da laifin satar Naira biliyan biyu na kudaden fansho.

Da yake sanar da hukncin, alkalin kotun, Mai Shari’a Okon Abang, ya ce Maina ya sace sama da Naira biliyan na ’yan fansho, “wadanda yawancinsu suka rasu ba tare da sun ci guminsu ba.

“Na samu wanda ake tunuha (Maina) laifuka na 2, 6, 9, 3, 7 da kuma na 10.”

Mai Shari’a Okon Abang ya kuma kama Maina da laifin ba wa wani ma’aikacin bankin Fidelity toshiyar baki ya bude masa asusun ajiya ba tare da cika ka’idoji ba, da kuma bude asusun ajiya da sunan wasu ’yan uwansa ba tare da saninsu ba.

A cikin asusun bankunan ne aka gano Naira biliyan 2.3, wanda kotun ta ce Maina ya kasa bayyana ta hanyar da ya samo kudaden, wadanda ta ce babu yadda za a yi ma’aikacin gwamnati mai irin matsayinsa ya mallake su.

Alkalin ya ce Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC), wadda ta gurfanar da Maina ta gabatar wa kotun gamsassun hujjoji da ke tabbatar da cewa Maina ya yi safarar haramtattun kudade Naira miliyan 171.

Maina dai zai yi zaman wakafin ne a lokaci guda, wanda ke nufin gaba daya shekara takwas zai yi a gidan yari; Tuni dai ya ki amsa laifukan.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Maina kan zargin aikata laifuka 12 na badakalar kudaden.

Daga cikin tuhume-tuhumen, ana zargin shi da amfani da kudaden satar, Naira biliyan biyu wajen sayen gidajen kashin kansa a Abuja da kuma safarar kudaden ta haramtacciyar hanya.

A watannin baya, tsohon shugaban kwamitin fanshon ya taba tserewa bayan kotu ta bayar da belin shi, bayan Sanata Ali Ndume ya tsaya masa domin ya samu ya kula da laifiyarsa.

Daga baya aka kamo shi a Jamhuriyyar Nijar, kotu ta sa aka ci gaba da tsare shi a gidan yari.

A watan Okotoba, kotu ta daure Faisal, dan Abdulrasheed Maina,  a gidan yari bayan ta same da laifi a halasta kudaden haram Naira miliyan 58.1.