✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta dakatar da mukabalar Abduljabbar da malaman Kano

Kotun ta kuma bukaci Gwamnatin Jihar Kano da malamin da su bi umarninta.

Wata Kotun Majistare dake Kano ta dakatar da mukabalar da aka tsara gudanarwa tsakanin Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara da sauran malaman addinin Musulunci a jihar Kano.

Kotun, yayin da take yanke hukunci ranar Juma’a ta kuma bukaci daukkan bangarorin guda biyu wato na Gwamnatin Jihar Kano da na malamin da su bi umarninta.

Tun da farko dai kotun ta jaddada dakatar da malamin daga ci gaba da wa’azi a jihar har zuwa lokacin da zata yanke hukunci a kan lamarin.

Bayan dawowar zaman kotun ranar Juma’a ne dai shari’ar ta dauki sabon salo bayan wani lauya, Barista Ma’aruf Yakasai ya garzaya gabanta da wannan bukatar.

Lauyan dai ya tsaya kai da fata cewa gabatar da mukabalar tamkar raini ne ga kotu kasancewar akwai wani hukuncin na kotu da ya hana malamin daga yin wa’azi a cikin jama’a ko kuma watsa duk wasu harkokinsa ta kafafen watsa labarai.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Muhammad Jibril ya umarci daukkan bangarorin guda biyu da su bi umarnin kotun sannan ya dage zaman kotun har zuwa 22 ga watan Maris domin ci gaba da sauraron karar.

Da yake tsokaci a kan lamarin, Kwamishinan Shari’a na jihar Kano, Barista Musa Lawal ya ce a matsayinsu na gwamnati mai bin doka da oda, za su girmama umarnin kotun.

Tun da farko dai Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da sanya ranar Lahadi, bakwai ga watan Maris a matsayin ranar gudanar da mukabalar a Fadar Sarkin Kano.