✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta dakatar da Secondus daga shugabancin PDP

Secondus dai ya tsaya kai da fata cewa ba zai sauka ba sai ya kammala wa’adinsa.

Rikicin jam’iyyar adawa ta PDP ya sake daukar sabon salo bayan da Babbar Kotun Jihar Ribas ta dakatar da Uche Secondus daga ci gaba da gabatar da kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

Secondus dai wanda ke fafutukar kare kujerar tasa na cikin tsaka mai wuya kan ko dai ya shirya babban taron jam’iyyar a watan Oktoba mai zuwa ko kuma ya sauka daga mukaminsa.

Shugaban dai ya tsaya kai da fata cewa ba zai sauka ba sai ya kammala wa’adinsa.

To amma a ranar Litinin, Mai Shari’a O. Gbasam ya dakatar da shi daga ci gaba da shugabancin PDP yayin da yake yanke hukunci a kan wata kara da wasu kusoshin jam’iyyar suka shigar.

Tun da farko dai Ibeawuchi Ernest Alex da Dennis Nna Amadi da Emmanuel Stephen da kuma Umezirike Onucha ne suka garzaya gaban kotun da bukatar dakatar da Secondus din.

Kazalika, alkalin ya kuma dakatar da Secondus daga jagorantar taron jam’iyyar ko dai a matakin mazaba ko na Karamar Hukuma har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci na karshe.

Da yake mayar da martani, Uche Secondus ya ce a shirye yake ya kare kansa idan wani ya kai shi gaban kotu.

A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Ike Abonyi ya fitar, Secondus ya ce, “Idan aka gurfanar da ni da jam’iyyarmu a gaban kotu, za mu kare kanmu.

“Ba ma jin tsoron kotu, PDP jam’iyya ce mai cike da tarihi kuma mallakin ’yan Najeriya, ta fi karfin kowanne mutum ko kuma kowacce irin kungiya, ciki har da ’yan-bani-na-iya.”