Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano, ta hana gayyata ko kama tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje domin bincikarsa kan zargin karbar cin hanci da rashawa.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis ce dai Hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta ce ta aika takardar sammaci ga tsohon gwamnan a kan ‘bidiyon dala’.
- Ruwan sama ya yi ajalin mutum 50 a Pakistan
- Hajiyar Najeriya mai shekara 66 ta rasu bayan kammala Aikin Hajji
Wata sanarwa da hukumar ta fitar, na cewa ta gayyaci Ganduje ne domin ya je ya wanke sunansa game da binciken da ake yi.
A shekarar 2017 ne, jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a intanet, ta fitar da jerin bidiyon da ke nuna wani mutum wanda ta yi zargin cewa Ganduje ne yake karbar damin daloli daga hannun wasu ’yan kwangila yana zubawa a aljihu.
Sanarwar ta ambato shugaban hukumar korafe-korafen, Muhuyi Magaji Rimin Gado yana cewa: “Na sa hannu a kan wata wasika don gayyatar shi, ya zo a yi masa tambayoyi a hukumar cikin makon gobe.
“Saboda abin da doka ta ce kenan kuma za mu bayar da dimbin damammaki don ya kare kansa.”
Wakilinmu ya ruwaito cewa a ranar Juma’a ce Ganduje ta bakin lauyansa B. Hemba ya gabatar da korafi a gaban alkalin Babbar Kotun da ke Kano, Mai Shari’a A.M. Liman, yana mai rokon ta shiga tsakaninsa da hukumar korafe-korafen.
Kan haka ne Kotun ta amsa rokon, inda ta dakatar da duk wani yunkuri na barazanar kamu, cin zarafi, ko tsare tsohon gwamnan tare da duk iyalansa da kuma wadanda ya bai wa mukami a gwamnatinsa har zuwa lokacin da za a saurari karar.
Daga cikin wadanda aka yi wa wannan kashedi kamar yadda Babbar Kotun ta ambato sun hada da rundunar ’yan sandan Najeriya, Babban Sufeton ’yan sanda na Kasa, Kwamishinan ’yan sandan Kano, Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Kano (SSS), Hukumar Sibil Difens, Atoni-Janar na Kasa, Atoni-Janar na Jihar Kano da kuma ita kanta hukumar korafe-korafen ta Kano wato PCACC.
Alkalin Kotun ya umarci duk wadanda aka ambato su yi wa umarnin biyayya har zuwa lokacin da za a soma sauraron karar a ranar 14 ga watan Yulin 2023.