✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta dakatar da nadin da Gwamnatin Kaduna ta yi wa Hakimai 77

A ranar Larabar da ta gabata ce wata Babbar kotu ta biyu a Jihar Kaduna da ke zamanta a GRA Zariya ta dakatar da nadin…

A ranar Larabar da ta gabata ce wata Babbar kotu ta biyu a Jihar Kaduna da ke zamanta a GRA Zariya ta dakatar da nadin da Gwamnan jihar ya yi wa Hakimai 77 bisa dalilin rashin bin umurnin kotu.

Da ya ke yanke hukunci akan karar da Gwamnatin Jahar Kaduna ta yi na korar wasu Hakimai tare da nada wasu guda 77, Mai Shari’a Kabiru Dabo ya ce, bangaran zartarwa ba ta da hurumin shiga harkar shari’a domin ba hurumin ta ba ne.

Ya ce gwamnati na tafiya ne bisa falle uku da bangaran zartarwa da Majalisa da kuma bangaran Shari’a, dan haka kowane bangare ya tsaya a matsayinsa.

Da wannan ne kotun ta umurci hakimai guda 77 da su daina amsa sunan hakimai, kuma ta umurci dukkan Hakiman da aka dakatar da su koma gundumominsu har sai an kammala shari’a, saboda haka kotun ta tsayar da ranar 16 ga Watan Janairun badi, dan ci gaba da sauraran karan.

Da yake tsokaci kan matakin da kotun ta dauka, lauyan Hakimai masu kara, Barista Yami Adekunle ya ce matakin da kotun ta dauka ya yi daidai domin ba wanda ya fi karfin kotu.

Shi kuwa lauyan Gwamnatin Jihar Kaduna, Barista Abdurahaman Suleman Haladu ya ce ba zai yi magana da ‘yan jarida ba, saboda bai sami umurnin yin hakan ba a halin yanzu.

Idan jama’a ba su manta ba, a bara ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta sallami hakimai 77, inda kuma daga bisani ta nada wasu sababbi, inda bisa dalilin haka ne su wadancan da aka sallama suka yi karar gwamnatin jihar, suna kalubalantar korar tasu da aka yi.