✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta dakatar da binciken da ake yi wa Sarkin Kano

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano ta umarci Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin hanci da Rashawa ta Jihar Kano da…

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano ta umarci Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin hanci da Rashawa ta Jihar Kano da ta dakatar da binciken da take yi wa Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II saboda korafin da Sarkin ya shigar gabanta.

Umarnin kotun ya shafi Hukumar Karbar Korafe korafe da Hana cin hanci da Rashawa da shugabanta Barista Muhyi Magaji Rimingado da Kwamishinan Shari”a koma Antony Janar na Jihar da kuma Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje.

Alkalin kotun Justis Lious Alagwua, ya umarci kowa ya tsaya a inda yake har sai kotun ta saurari korafin na Sarkin wanda kuma ta sanya ranar 18 ga watan Maris don sauraro.

Hukumar Karbar Korafe Korafe da Yaki da Cin hanci da Rashawa ta nemi Sarkin Kano, da ya bayyana a ofishinta a ranar Litinin din makon gobe don amsa wasu tambayoyi kan tuhume-tuhumen da take yi masa da suka hada da sayar da wasu filaye a Gandun Sarki da ke Hotoro da sauransu.