✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta bada umarnin kwace gidajen Saraki na Legas

Wata babbar kotu da ke garin Ikoyi a jihar Legas, ta bada umarnin kwace gidaje biyu na tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki, don…

Wata babbar kotu da ke garin Ikoyi a jihar Legas, ta bada umarnin kwace gidaje biyu na tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki, don mallakawa gwamnatin tarayya.

Wadannan gidajen suna yankin garin Ikoyi da ke birnin Legas. Kotun ta bada wannan umarnin ne bayan lauyan Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) Nnaemeka Omewa, ya gabatarwa kotun gidajen mallakar Saraki, gidajen suna lamba na 17A layin McDonald, a Ikoyi Karamar Hukumar Eti Osa, jihar Legas. Ana zargin tsohon Shugaban Majalisar da mallakar gidajen ta haramtacciyar hanya.

Hukumar EFCC tana tuhumar Bukola Saraki da mallakar gidajen lokacin yana Gwamnan jihar Kwara, inda ya cire kudi Naira Biliyan 12 daga cikin asusun gwamnatin jihar don sayan wadannan gidajen.