✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta bada belin Adoke kan Naira miliyan 5

Babbar Kotun Birnin Tarayya Abuja da ke zama a Gwagwalada ta bayar da belin Tsohon Ministan Shari’a kuma Atoni Janar na Najeriya, Mohammed Adoke (SAN)…

Babbar Kotun Birnin Tarayya Abuja da ke zama a Gwagwalada ta bayar da belin Tsohon Ministan Shari’a kuma Atoni Janar na Najeriya, Mohammed Adoke (SAN) kan Naira miliyan 50.

Alkalin kotun, Mai shari’a Abubukar Idris, ya kuma bukaci tsohon Ministan ya kawo wanda zai tsaya masa domin beli, wanda shi ma ya mallaki kudin da ya kai na belin.

Haka kuma an bada sauran mutum biyu da ake tuhuma tare da shi beli.

A bangaren wanda ake tuhuma na biyu mai suna Abubakar Aliyu, shi ma an bada belinsa ne kan Naira miliyan 50, sai na ukunsu, Rasky Gbinigie wanda aka ba belinsa kan Naira miliyan 10.

Duk kansu, kotun ta bukaci masu belinsu su kasance mazauna Abuja, kuma suna da kadara a garin Abuja.

Akwai wasu sharudan belin da ba a ji da kyau ba har zuwa lokacin hada wannan labarin domin ba a jin alkalin sosai.

A yanzu dai an dage sauraron karar zuwa 26 da 27 ga watan Maris 2020.

Alkalin ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda masu kara da wadanda ake kara suka zabi lokaci mai tsawo.

“Na zata zuwa mako mai zuwa za mu fara. Amma tunda duk kun amince, shi kenan,” in ji shi.