Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da ummarnin aikewa da sammaci da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gurfana a gabanta cikin kwanaki biyar don ya bayar da shaida a shari’ar tsohon mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Olisa Metuh.
Mai shari’a Okon Abang ya yanke hukuncin cewa kotun ba za ta zargi tsohon shugaban kasar ba saboda rashin halartar kotun jiya (Laraba).
Ya kara da cewa ka’idojin kotun suna da mutukar muhammanci a kowace shari’a da kotun ke yi.