✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba da belin ’yan uwa a N40,000 kan satar kaji 3

Kotu ta bayar da belin wadanda suka saci kaji uku a nan N20,000 kowannensu

Wata kotun majistare ta bayar da belin wasu ’yan uwan juna a kan N20,000 kowannensu bayan gurfanar da su a kan satar kaji uku.

Kotun ta dauki matakin ne bayan an garfanar da matasan su biyu kan zargin da satar kaji uku da kudinsu ya kai Naira 45,000 a yankin Okebola a Jihar Ekiti.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Celeb Leramo, ya shaida wa kotun da ke zamanta a Ado-Ekiti cewa a ranar 4 ga watan Nuwamba da misalin karfe 2 na rana wadanda ake tuhumar suka sace kajin uku mallakin Akogun Yemisi.

Lauyan wadanda ake kara, Barista Gnenga Ariyibi, ya bukaci kotun da ta bayar da belin su.

Alkalin kotun, Saka Afunso, ya bayar da belin kowannen su akan kudi N20,000 da gabatar da mutum daya da zai tsaya masa, sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba.