✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta aike da mutumin da ya sayar da mahaifinsa ga matsafa kan N1.8m kurkuku

Mutumin ya sayar da mahaifin nasa ne mai shekara 82 ga matsafa

Wata kotun majistare da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, ta tisa keyar wasu mutum uku zuwa gidan gyaran hali, saboda samun su da laifin sacewa da kashe wani tsoho mai shekara 82.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Bankole Okuwasanmi ne ya bayar da umarnin aike wa da Sunday Obasuyi mai shekara 42 da dan marigayin, Akinniyi mai shekara 51, sai kuma Bobafe Sunday mai shekara 51, zuwa gidan gyaran hali.

Ya ce za su ci gaba da zama a tsare har zuwa lokacin da Daraktan Gabatar da Kara (DPP) na Jihar zai ba da shawara kan mataki na gaba.

Tun da farko, mai shigar da kara, Insfekta Akinwale Oriyomi, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun hada baki tare da sace mutumin ranar 1 ga watan Fabraiun da ya gabata.

Akinwale ya ce an sace dattijon ne wajen misalin karfe 11:00 na safe a gidansa da ke Agbado-Ekiti a Karamar Hukumar Gbonyin ta Jihar. Ya ce bayan wasu ’yan makonni, an tsinci gawar mutumin a wani dan karamin kabari.

Mai shigar da karar ya kuma shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma na farko, Sunday, ya hada baki da Akinniyi, inda ya sayar masa da mahaifi ga wanda ake tuhuma na uku, Bobafe, wanda matsafi ne a kan kudi Naira miliyan daya da dubu 800.

Ya ce laifukan sun saba da sassa na 280 da 279 da 234 na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Ekiti na shekara ta 2021.