Babbar Kotun Shariar Musulunci da ke zamanta a Gama PRP a Jihar Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Nura Yusuf Ahmad ta bayar da umarnin tsare fitacciyar ’yar Tikttok Murja Ibrahim Kunya a gidan gyaran hali bisa zargin ta da aikata ayyukan fitsara da badala da kuma tayar da hankalin jama’a.
Mai gabatar da kara Aminu Abdullahi ya shaida wa kotun cewa Hukumar Hisbah ce ta kama Murja Kunya sakamakon samun korafe-korafe daga al’ummar yankin Tishama inda Murja ke zaune, cewa tana tayar musu da hankali tare da tsoratar da su ta hanyar kawo musu bata-gari da tsakar dare.
Haka kuma wacce ake tuhumar tana amfani da kafafen sada zumunta tana yada badala da fitsara, baya ga koyar da karuwanci da take ga ’ya’yansu.
“Ke da kanki a cikin wani bidiyon da ya karade shafukan zumunta na zamani kin bayyana cewa ke ce shugabar duk wata karuwa ko ’yar kwalta da ke Jihar Kano,” in ji mai gabatar da kara.
A cewarsa, laifukan da ake zargin ta sun saba da sashe na 341 da 275 da 227 na Kundin Pinal Kod.
Sai dai wacce ake tuhumar ta musanta laifukan da ake zargin ta da su.
Lauyanta, Barista Aliyu Umar Faruk, ya nemi kotun da ta bayar da belin wacce ake tuhumar, rokon da kotun ta ki amincewa da shi.
Kotun ta yi umarni da a tsare wacce ake tuhumar a gidan gyaran hali har zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu 2024, don bayyana ra’ayinta game da batun belin.