Wata kotun majistare da ke birnin Maiduguri na Jihar Borno ta yanke wa Farfesa Abdulfattah A. Aboaba na Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari.
Kotun ta kuma bai wa Farfesa zabin biyan tarar Naira dubu 10 bisa samunsa da laifin razanar da wani abokin aikinsa, laifin da ya ci karo da sashe na 397 na kundin laifuffuka.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wani kwafin hukuncin da kotun ta yanke kuma aka raba wa manema labarai ranar Juma’a a Maiduguri.
“An yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin ne bayan wata wasikar amincewa da kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno ya samu a ranar 3 ga Nuwamba, 2021 daga Farfesa Shehu Mustapha Liberty, yana zargin ana yi wa rayuwarsa barazana, lamarin da ya kai ga bincike da kuma shari’ar da Kotun Majistare ta yi.”
A yayin shari’ar dai, ’yan sanda da masu kara sun gabatar da shaidu a gaban kotu, inda alkali ya bai wa lauyan wanda ake tuhuma damar bin diddigin dukkan shaidun masu gabatar da kara domin tabbatar da gaskiyar zargin.
Da yake yanke hukunci a kan wanda ake tuhumar, Mai Shari’a Alhaji Saleh Isaya yi la’akari da korafin lauyan wanda ake tuhuma, wanda ya nemi a yi wa wanda yake karewa sassauci kasancewa yana da hali mai kyau.
Alkalin ya yanke wa Farfesan hukunci cin sarka ta shekara biyu a Gidan Dan Kande tare da ba shi zabin biyan tarar N10,000 kacal.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, tunda farko dai Farfesa Abdulfattah A. Aboaba da Farfesa Shehu Mustapha Liberty sun samu sabani ne a yayin wani taron Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU reshen Jami’ar ta UNIMAID da aka gudanar a ranar 29 ga watan Oktoban 2021.