Kotun daukaka kara ta Abuja ta sake komawa da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki zuwa Kotun da’ar Ma’aikata domin a sake yi masa shari’a a kan zargin rashin gaskiya wajen bayyana kadarorinsa, inda kotun ta ce wankar da kotun ta yi masa a baya bai wanku ba.
Gwamnatin Tarayya ce ta daukaka kara bayan da Kotun da’ar Ma’aikatan (CCT) ta wanke Shugaban Majalisar Dattawan a farkon shekarar nan.
Kotun da’ar Ma’aikatan ta yi watsi da daukacin tuhume-tuhume 18 da suka shafi rashin bayyana gaskiya lokacin da yake bayyana kadarorinsa ga Hukumar da’ar Ma’aikata (CCB).
A zamanta na ranar Talata, kotun ta yanke hukuncin cewa Sanata Saraki bai bayar da gamsasshiyar amsa kan uku daga cikin tuhume-tuhume 18 da aka yi masa ba.
Alkalai uku da suka saurari karar a zaman kotun a karkashin Mai shari’a Tinuade Akomolafe-Wilson, sun yi watsi da sauran tuhume-tuhume 15 da Gwamantin Tarayya ke yi wa Saraki.
A martaninsa Sanata Bukola Saraki ya ce amincewa da bukatarsa ta ba ya da laifi a kan zarge-zarge 15 ya tabbatar da rashin laifinsa, kamar yadda Kakakinsa Yusuph Olaniyonu ya fadi a wata sanarwa.
Lauyoyin Saraki da na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati sun nuna cewa za su daukaka kara a kan hukuncin zuwa Kotun koli.
Lauyan Hukumar EFCC, Rotimi Jacobs, ya ce zai yi nazari kan hukuncin kotun kafin ya yanke shawara kan matakin da zai dauka na gaba.