Koriya ta Arewa ta zargi Amurka da kara rura wutar yakin Gabashin Turai a sakamakon taimaka wa Ukraine da ta yi da makaman yaki da sunan kare kanta daga mamayar Rasha.
Koriya ta Arewa ta soki matakin Amurka na taimaka wa gwamnatin Kyiv da tankunan yaki da ta ce, taimakon ba zai yi tasiri ba illa ya kara rura wutar rikicin yakin da ke ci a gabashin Turai.
- NRC ta dakatar da zirga-zirgar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
- Magidanci ya yi karar matarsa kan kara aure a sirrance
Wasu rahotanni na cewa wadannan kalaman na kanwar Shugaba Kim Jong Un, wato Kim Yo Jong, sun tabbatar da zargin da aka jima ana yi wa Koriya ta Arewa na mara wa Rasha baya a mamayar Ukraine.
Haka kuma dama wannan ba shi ba ne karon farko da kasar ke sukar Amurka da zama kanwa uwar gami a rikicin makwabtan biyu.
Duk wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rahotannin suka tabbatar da cewa Rasha na kara zafafa hare-haren da ta ke kai wa a Arewa da Gabashin Ukraine,
A daya bangaren, kasashen Tarayyar Turai sun dauki mataki na tsawaita takunkumin karya tattalin arzikin da suka sanya wa Rasha da wasu karin watanni shida a taron da suka yi a ranar Juma’ar, takunkuman sun hadar da tazgaro ga hada-hadar mai da musayar kudade da wasu haramcin da suka shafi Shugaba Vladimir Putin kai tsaye.