Kasashen Musulmai na ci gaba da yin Allah wadai da kasar Sweden bayan wata zanga-zangar da masu tsattsauran ra’ayi suka gudanar a cikinta, ciki har da kona Alkur’ani.
An dai gudanar da zanga-zangar ce a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da ke Stockholm, babban birnin Sweden din.
- 2023: Babu dan Najeriyar da ya san ciwon kansa da zai zabi APC – Gwamnan Bayelsa
- Jaruman Kannywood da aka daina jin duriyarsu
Tuni dai gwamnatin Turkiyya a ranar Asabar ta sanar da soke ziyarar da aka shirya Ministan Tsaron Sweden din zai kai kan nuna rashin amincewar da ta nuna da shigar Sweden din Kungiyar Ƙawancen Tsaro ta NATO.
Rasmus Paludan, jagoran jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi ta Hard Line da ke kasar Sweden ne dai ya jagoranci kona Alkur’anin.
A watan Afrilun bara, sanarwar da Rasmus din ya fitar kan aniyarsa ta kona littafin mai tsarki a cikin watan Ramadan, ta jawo cece-ku-ce da zanga-zanga mai zafi a kasar.
Sai dai yayin zanga-zangar wacce ’yan sanda suka kewaye shi, Rasmus ya cinna wa Alkur’anin wuta da leta, bayan y shafe tsawon awa daya yana caccakar Musulunci a Sweden.
Sai dai kimanin mutum 100 ne su ma suka taru a gefe don yin zanga-zangar rashin amincewa da matakin na Rasmus.
Mutumin dai ya ce, “Idan kana tunanin mutane ba su da ’yancin fadin albarkacin bakinsu, to ya kamata ka nemi wata duniyar ka koma rayuwa a cikinta.”
Amma dai nan take Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta mayar masa da martani a cikin wata sanarwa, inda ta bayyana matakin a matsayin takalar fada da tsagwaron nuna tsanar Musulunci.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu, ya kalubalanci hukumomin Sweden kan kin hana zanga-zangar, inda ya bayyana ta a matsayin ta nuna kin jinin Musulunci, ba ta fadin albarkacin baki ba.
Kasashen Larabawa da dama, ciki har da Saudiyya ma sun bi sahu wajen yin Allah wadai da matakin na Sweden.