✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kokuwar gargajiyar da ake yi a Abuja ta watse

Wasan kokuwar gargajiya da ake fafatawa a gidan wasa na Maishanwa da ke daki-Biyu a Abuja ta watse a daidai lokacin da ake shirin fafata…

Wasan kokuwar gargajiya da ake fafatawa a gidan wasa na Maishanwa da ke daki-Biyu a Abuja ta watse a daidai lokacin da ake shirin fafata gasar lashe rago da babur da aka shirya farawa a jiya Alhamis. Ana fafata gasar kokuwar ce a tsakanin ’yan wasan kokuwar da suka fito daga sassan Najeriya da kuma na Jamhuriyyar Nijar.

’Yan wasan kokuwa fiye da 50 ne suka fara fafatawa a gidan wasan na Maishanawa, inda 32 suka fito daga Nijar da sai kuma 20 suka fito daga Najeriya.

Manyan ’yan wasa kokuwa daga Najeriya da suka hada da Bashari Zariya da Murtala Yobe da Musa Biski da sauransu da kuma takwarorinsu na Jamhuriyyar Nijar da suka hada da Kabiru Ghali da danguda Alhaji da Adamu dan Malam da Kwado Sule da Rufa’i Goga da Aminu Yaro da sauransu ne suka hallara a gidan wasan, sai dai kuma wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, a daidai lokacin da ake shirin fara gasar lashe rago, sai aka nemi ’yan kokuwa daga Najeriya sama da kasa aka rasa.

Kafin nan a kokuwar da aka fafata a ranar Lahadin da ta gabata, Murtala Yobe ya kada Kwado Sule, daga Jamhuriyyar Nijar yayin da Kabiru Ghali daga Nijar ya kayar da Musa Biski daga Najeriya. Sannan Musa Biski na Najeriya ya kayar da Rufa’i Goga daga Nijar a fafatawar da suka yi. 

Sauran ’yan kokuwa da dama sun fafata inda aka rika samun kaye da kuma yin canjaras. Kuma kafin watsewar kokuwar a kullum ana samu fafatawa sau 20 zuwa 30 tare da yin kaye ko canjaras a tsakanin ’yan wasan kokuwar.