✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kofin FA:  Yau Arsenal za ta kece raini da Man United

A yau Juma’a ce kulob din Arsenal zai hadu da na Man United a wasa zagaye na hudu na gasar cin Kofin Kalubale na Ingila (FA)…

A yau Juma’a ce kulob din Arsenal zai hadu da na Man United a wasa zagaye na hudu na gasar cin Kofin Kalubale na Ingila (FA)

Za a yi wasan ne a filin wasan Arsenal na Emirates da misalin karfe 8:55 na dare agogon Najeriya.

Ana sa ran gidajen kallon kwallo a Najeriya su cika makil don ganin yadda wasan zai kaya musamman magoya bayan kungiyoyin biyu.

Tarihi ya nuna kulob din Arsenal ne ya fi daukar wannan kofi, inda ya lashe har sau 13 yayin da Manchester United ce ke biye inda ya dauka sau 12.

Ke nan idan Arsenal ta samu nasarar lashe kofin a bana, za ta hada 14 ke nan idan kuma United ta lashe za ta kamo Arsenal ke nan inda  za ta hada na 13.

Arsenal dai ta taba lashe kofin ne a 1929/1930 sai a 1935/1936 sai 1949/1950 sai 1970/1971 sai 1978/1979 sai 1992/1993 sai a 1997/1998 sai shekarar 2001 /2002 da 2002/2003 da 2004/2005 da 2013/2014 da 2014/2015 sai kuma shekarar 2016/2017.

Manchester United kuma ta lashe ne a shekarun 1908/1909 da 1947/1948 da 1962/1963 da 1976/1977 da 1982/1983 da 1984/1985 da 1989/1990 da 1993/1994 da 1995/1996 da 1998/1999 da shekara 2003/2004 sai kuma a  2015/2016.