Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka CAF a madadin FIFA ta fitar da jadawalin wasannin neman gurbi a gasar Kofin Duniya bangaren kasashen Afrika.
Jadawalin wanda CAF ta fita a ranar Alhamis a birnin Abidjan na kunshe da kasashe 54 wadanda aka rarraba rukunnai 9 da za su fafata a wasannin gida da waje don fitar da zakaru a cikinsu.
- Abubuwan da suka kamata a sani kan cutar Diphtheria da take yaduwa a Najeriya
- WHO ta tallafa wa yara 6,000 da abinci mai gina jiki a Borno
Jadawalin ya nuna cewa rukunin A na kasashen na kunshe da Masar da Burkina Faso da Guinea Bissau kana Saliyo sai Habasha sannan Djibouti.
A rukunin B akwai kasashen Senegal da jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo kana Mauritania sai Togo da Sudan da kuma Sudan ta kudu.
Bangaren rukunin C kuwa ya kunshi kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu kana Benin da Zimbabwe sannan Rwanda da Lesotho.
Rukunin D na dauke da kasashen Kamaru da Cape Verde da Angola da Libya sannan Eswatini sai Mauritius.
Rukunin E kuwa akwai kasashen Morocco da Zambia da Congo Brazzaville da Tanzania sai Jamhuriyar Nijar kana Eritrea.
Rukunin F na kunshe da Ivory Coast da Gabon da Kenya da Gambia sannan Burundi sai tsibirin Seychelles.
A Rukunin G akwai kasashen Algeria da Guinea da Uganda da Mozambique kana Bostwana da Somalia.
Jadawalin na CAF na nuna cewa a rukunin H akwai Tunisia da Equatorial Guinea kana Namibia sannan Malawi da Liberia da kuma São Tome and Principe.
Rukunin I kuma na karshe a wannan jadawali na dauke da kasashen Mali da Ghana sannan Magadascar sai Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya sannan tsibirin Comoros kana Chad.