✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kofin Carling: An cire kulob din Chelsea da Arsenal da na Man U

A ranar Talatar da ta wuce ne aka fitar da kulob din Chelsea da kuma na Arsenal daga gasar cin kofin Kalin da aka fi…

A ranar Talatar da ta wuce ne aka fitar da kulob din Chelsea da kuma na Arsenal daga gasar cin kofin Kalin da aka fi sani da Capital One Cup na Ingila. Sannan a shekaranjiya Laraba kuma kulob din Middlesbrough ya fitar da na Manchester United. Middlesbrough ta fitar da United da ci 3-1 ne a bugun fanariti.
  Ita dai Chelsea mai rike da kofin, kulob din Stoke City ne ya fitar da ita bayan an tashi wasa ci 1-1 a bugun fanariti.  A bugun fanariti ne aka fitar da kulob din da ci 5-4.  Wannan shi ne karo na biyu a jere da kulob din yake shan kashi bayan da kulob din West Ham United ya doke shi a gasar rukunin firimiya na Ingila a ranar Lahadin da ta wuce da ci 2-1. A yanzu kulob din ya samu rashin nasara a wasanni 9 da ya yi a kakar wasa ta bana da hakan ta sa ya kasance a sahun koma baya.
A bangaren kulob din Arsenal kuwa, kulob din ya sha kashi ne a wajen Sheffield Wednesday a gasar cin kofin Kalin da ci 3-0.  Da yawa daga magoya bayan kulob din sun dauka Arsenal za ta lallasa na Wednesday ne amma sai aka samu akasin haka inda reshe ya juye da mujiya.  Kuma wani abu mai tayar da hankali shi ne yadda zaratan ’yan kwallon Arsenal biyu Aled Odlade-Chamberlain da Theo Walcott suka ji rauni, al’amarin da ya sa ba za su buga wa kulob din wadansu wasanni ba. Yanzu dai an cire wadannan kulob uku kenan daga gasar  sai kuma badi idan Allah Ya kaimu.