A safiyar yau Juma’a ne Mai Horas da ‘Yan Wasan Kwallon Kafar kasar nan, Super Eagles, Mista Sunday Oliseh ya sanar da yin murabus daga kan mukaminsa.
Kociyan ya sanar da yin murubus din ne a wani takaitaccen sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya ce “na dauki wannan mataki ne saboda saba ka’adojin kwantiragina da kuma rashin goyon baya da yake samu tare da kin biyan hakkokina da na mataimakana da kuma sauran ‘yan wasana.”