✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kocin Madrid Ancelotti ya nuna bacin rai a kan ’yan kwallonsa

Kocin kulob din Real Madrid da ke Sifen Carlo Ancelotti ya koka da yadda ’yan kwallonsa ba sa nuna kwazo a gasar rukunin La-Liga a…

Kocin kulob din Real Madrid da ke Sifen Carlo Ancelotti ya koka da yadda ’yan kwallonsa ba sa nuna kwazo a gasar rukunin La-Liga a ’yan kwanakin nan, bayan kulob din ya yi kunnen doki a gida da ci 1-1 da na billareal a ranar Lahadin da ta wuce.

Kocin ya nuna bacin ransa ne jim kadan bayan an tashi wasan. A daidai minti na 52 ne dan kwallon Madrid Cristiano Ronaldo ya zura kwallo a ragar billareal a bugun daga kai sai mai tsaron gida (fanariti) amma dan kwallon billareal mai suna Gerard Moreno ya fanshe a daidai minti na 64.
Wannan shi ne karo na farko da kulob din Madrid ya yi kunnen doki a gida tun lokacin da aka fara gasar ta La-Liga.
Yanzu ya rage saura maki biyu a tsakanin kulob din da na FC Barcelona a teburin gasar. A ranar 22 ga wannan watan ne ake sa ran kungiyar Madrid za ta kece raini da ta FC Barcelona a wasan da ake wa lakabi da El-Classico.