✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kocin Kano Pillars ya ajiye aiki

Jabiru A. Hassan, a Kano da Ahmed Garba Mohammed Mai horar da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Muhammad Babaganaru ya ajjiye aikin…

Jabiru A. Hassan, a Kano da Ahmed Garba Mohammed

Mai horar da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Muhammad Babaganaru ya ajjiye aikin horar da kungiyar saboda gazawar da kungiyar ta yi na tabuka wani abin kirki a kakar wasa ta bana.
A cikin wata sanarwa da mai horar da ’yan wasan ya bayar, ya bayyana cewa ya ajiye aikin horar da kungiyar ne saboda halin da ta shiga na rashin cimma nasarar da ake bukata a gasar Firimiya ta Najeriya.
A ranar Lahadin da ta gabata ce kungiyar  Kano Pillars ta  buga wasanta na 36 a tsakaninta da kungiyar kwallon kafa ta  Niger Tornadoes inda aka tashi kunnen doki da ci 1-1,  wanda hakan ya sanya Kano Pillars ta tashi da maki 52  kuma ta gama a mataki na bakwai.  
Wakilinmu ya tattauna da wadansu daga cikin magoya bayan kungiyar ta Kano Pillars dangane da yadda gasar ta bana ta kasance.
Auwalu Soja Kwa, wani matashin dan kwallo kuma mai goyon bayan kungiyar ta Kano Pillars ya ce duk da halin da kungiyar ta shiga, ’yan wasanta sun taka rawar gani a duk wasannin da suka buga, sannan su kansu jami’an kungiyar sun yi aiki tukuru har zuwa karshen wasannin.
Shi ma mai horar da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Ganduje  Boys da ke karamar Hukumar Gwarzo, Mustapha Umar Tallo ya ce gwamnatin Ganduje ta bai wa kungiyar dukkan goyon bayan da take bukata.
 “Shugaban kungiyar Kano Pillars, Kabiru Baita shi ma ya yi nasa kokarin kamar yadda mai horar da ’yan wasan  Babaganaru ya yi  da  su kansu ’yan wasa  amma ba a cimma nasara ba, don haka sai a bullo da wasu hanyoyi na inganta kungiyar ta yadda za ta kara karfi don tunkarar wasannin gaba,” inji shi.
Kusan duk mutanen da Aminiya ta zanta da su sun yi kira ne ga gwamnatin Jihar Kano ta kara karfafa kungiyar Kano Pillars tare da kara wa shugabanta  Alhaji Kabiru Baita damar tsara yadda al’amuran kungiyar za su inganta musamman ganin cewa mutum ne wanda ya san makamar aikin bunkasa kungiyar kwallon kafa a kowane mataki.
Sai dai kulob din na Pillars tuni ya bayar da sanarwar yunkurin daukar sabon koci nan ba da dadewa ba.