✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kocin Jamus zai maye gurbin Zidane a Madrid

Rahotanni da ke fitowa daga Sifen sun nuna kulob din Real Madrid na Sifen ya fara zawarcin Kocin Jamus Joacdhim Low don maye gurbin Zinedine…

Rahotanni da ke fitowa daga Sifen sun nuna kulob din Real Madrid na Sifen ya fara zawarcin Kocin Jamus Joacdhim Low don maye gurbin Zinedine Zidane a karshen kakar wasa ta bana.

Joachin Low dan shekara 57 shi ya jagoranci Jamus ta lashe kofin kwallon kafa na duniya a Brazil a shekarar 2014. 

Sannan Low kwararren koci ne inda ya horar da kulob daban-daban a Jamus ciki har da na Stuttgart.

Rahoton da kafar yada labaran wasanni  a Sifen Dairio Gol ta fitar a ranar Talatar da ta wuce an nuna kulob din Real Madrid ya fara yunkurin maye gurbin kocinsa na yanzu Zinedine Zidane ne ganin yadda kulob din yake tangal-tangal a kakar wasa ta bana.

Kawo yanzu kulob din FC Barcelona ya ba na Madrid tazarar maki 19 ne a gasar La-Liga ta Sifen kuma Madrid ta samu nasara a wasa daya ne kacal daga wasanni biyar da ta yi a ’yan kwanakin nan.

Kamar yadda rahoton ya nuna idan Low ya karbi ragamar kulob din Madrid zai sallami ’yan kwallo masu yawa ciki har da Gareth Bale da Kareem Benzema da Lukas Modric da Cristiano Ronaldo don maye gurbinsu da zaratan ’yan kwallo.  Sai dai kocin yana tunanin ba zai sallami Cristiano Ronaldo ba don zai hada shi da zaratan ’yan kwallo ne.

Kocin ya nuna zai sayo Neymar daga kulob din PSG na Faransa da Harry Kane na kulob din Tottenham da ke Ingila da golan Chelsea Thibout Courtious da kuma dan kwallon kulob din RB Leiping na Jamus Tino Werner don ya karfafa ’yan wasan Madrid.

Zinedine Zidane dai shi ne kocin da ya taimaki kulob din Madrid wajen lashe kofuna da dama a kasa da shekara biyu, kuma ya kafa tarihin lashe wa kulob din Gasar Zakarun Kulob na Turai (Champions League) sai biyu a jere.  Sai dai kawo yanzu Zidane yana fuskantar kalubale ganin yadda Madrid ta samu nasara ne a wasa daya kacal daga wasanni biyar da ta yi.