✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kocin Eagles zai gayyato bictor Anicehebe

Rahotanni da ke fitowa sun nuna kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Gernot Rohr ya fara yunkurin gayyato dan Najeriya da ke buga wa…

Rahotanni da ke fitowa sun nuna kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Gernot Rohr ya fara yunkurin gayyato dan Najeriya da ke buga wa kulob din Sunderland na Ingila kwallo bictor Anichebe.

Rabon da Anichebe ya yi wa Super Eagles kwallo tun a shekarar 2012. Hankalin kocin Eagles ya karkata a kan dan kwallon ne bayan ya lura tauraruwarsa tana haskakawa a gasar firimiyar Ingila ta bana.
Kocin ya ce “ina sa ran zan gayyato bictor Anichebe a wasan da Super Eagles za ta yi na gaba, don na fahimci yana da hazaka”.
bictor Anichebe dai ya taba buga wa kulob din Eberton na Ingila kwallo kuma tun a shekarar 2012 kococin da suka horar da Super Eagles suka daina gayyatarsa saboda rashin kwazo amma yanzu da tauraruwarsa take haskakawa ta sa sabon koci dan asalin Jamus Gernot Rohr ya fara yunkurin gayyatar sa.