✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko za a iya magance Boko Haram a makonni shida? 2

Kowa dai a yau ya san labarin an dage zabe zuwa makonni shida masu zuwa, bisa dalilin cewa jami’an tsaro za su tunkari ’yan Boko…

Kowa dai a yau ya san labarin an dage zabe zuwa makonni shida masu

zuwa, bisa dalilin cewa jami’an tsaro za su tunkari ’yan Boko Haram

domin kawar da su gaba daya. Abin tambaya a nan, shin ko za a iya

magance matsalar ta Boko Haram cikin makonni shida masu zuwa? Ga abin

da mutane suka ce, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:

Za su iya a makonni shida
– Ibrahim Muhamamd
Ibrahim Muhammad: “A ra’ayina sojojin za su iya yakar ’yan Boko Haram

cikin wannan wa’adi. Abin da ya kamata ’yan Najeriya mu yi shi ne

addu’ar Allah Ya ba su nasarar kawo karshen wannan musiba da ta

addabe mu ba wai mu rika karyata su ba. A kullum kyakkyawan zato ya

kamata mu yi wa shugabanninmu.”