✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ya dace sarakunan gargajiya su rika murabus idan sun tsufa?1

A wasu kasashe, sarakunan gargajiya sun fito da salon yin murabus suna nada ’ya’yansu a gadon sarauta tun suna raye, Sarkin katar da wata sarauniya…

A wasu kasashe, sarakunan gargajiya sun fito da salon yin murabus suna nada ’ya’yansu a gadon sarauta tun suna raye, Sarkin katar da wata sarauniya a Swiziland da kuma wani sarki a kasar Beljiyom, duk sun yi murabus, suka nada magadansu tun suna da rai. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace sarakunanmu na gargajiya su yi koyi da wannan salon? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:

Ya dace su rika murabus in sun tsufa – Buhari Zakari

Alhaji Buhari Zakari Kafe Gada Wazirin Kafe: “A gaskiya ya dace sarakunan gargajiya su rika yin ritaya suna bar wa ’ya’yansu sarauta tun suna raye.
Duk sarkin da ke kan karagar mulki, in har ya tsufa, ta yadda ba zai iya tafiyar da harkokin mulkin al’ummarsa ba; yana da kyau ya sauka ya barwa dansa ko kaninsa ko kuma wani da ya dace ya jagoranci wannan al’umma tasa.
Idan aka yi haka, an yi adalci. Idan tsufa ya kama mutum babu yadda za a yi ya iya gudanar da harkokin
mulkin al’ummarsa. Idan kuwa haka ne, mene ne amfanin zaman mutum a kan sarauta? Saboda haka rashin adalci ne a ce mutum bayan ya tsufa ya ci gaba da zama a kan sarauta.”