✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ya dace a takaita yawan jam’iyyu zuwa biyu a Najeriya?5

Idan ana batun al’amuran siyasa a Najeriya, musamman tun daga 1999 zuwa yau, akwai jam’iyyu masu yawa. Wasu na ganin cewa ya dace a takaita…

Idan ana batun al’amuran siyasa a Najeriya, musamman tun daga 1999 zuwa yau, akwai jam’iyyu masu yawa. Wasu na ganin cewa ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu kacal, a yayin da wasu kuma ke ganin cewa ya dace a bar su da yawa, domin al’umma su samu zabi. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu kadai ko kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

Ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu
– Malam Abubakar
Malam Abubakar Abdullahi Musa: “Ya dace jam’iyyu su koma guda biyu, muddin idan yin hakan zai kawo ci gaban kasa da kwanciyar hankali da bunkasar tattalin arziki da ilimi da lafiya da tituna da sauran kayan more rayuwa. Amma idan hakan ba zai samar da abubuwan da na lissafa ba, to barin jam’iyyun yadda suke shi ya fi.”