✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ya dace a takaita yawan jam’iyyu zuwa biyu a Najeriya?

Idan ana batun al’amuran siyasa a Najeriya, musamman tun daga 1999 zuwa yau, akwai jam’iyyu masu yawa. Wasu na ganin cewa ya dace a takaita…

Aminu Abdullahi GusauIdan ana batun al’amuran siyasa a Najeriya, musamman tun daga 1999 zuwa yau, akwai jam’iyyu masu yawa. Wasu na ganin cewa ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu kacal, a yayin da wasu kuma ke ganin cewa ya dace a bar su da yawa, domin al’umma su samu zabi. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu kadai ko kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

Ya kamata jam’iyyun su yi yawa – Aminu Abdullahi
Aminu Abdullahi Gusau: “Ni a ra’ayina, bai dace a yi jam’iyyu guda biyu ba kawai a Najeriya, ya kamata su wuce haka nan saboda ai dimukuradiyya aka ce ana yi. Don haka ya dace a bai wa kowa ’yancinsa na gudanar da siyasa yadda ya dace da kuma ra’ayin al’ummar kasa. Yin kaka shi ne yake kawo gogewa da sanin siyasar duniya amma idan jam’iyyu suka zama guda biyu kacal, to akwai kuraye wadanda suke nuna sun fi kowa iyawa. Su ne suke kashe siyasar kasar nan, ba su son baki sai wadanda za su danne don su yi masu bauta. Don haka bai dace ba, gara a same su da yawa.”