✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya?5

A halin da ake ciki, dalibai sun yi yawa a Najeriya, har ta kai ma a kowace shekara daliban da suka cancanci shiga jami’a ba…

A halin da ake ciki, dalibai sun yi yawa a Najeriya, har ta kai ma a kowace shekara daliban da suka cancanci shiga jami’a ba sa samun gurabe. Shin ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Ya kamata a kara yawan jami’o’i – Mustapha Muhammad
Mustapha Muhammad: “kari ko kafa sabbin jami’oi a kasar nan zai taimaka wajen ba matasa samun gurbin yin karatu, musamman idan aka yi la’akari da yawan matasa da ke kammala karatunsu na sakandire. Amma akwai bukatar a inganta ilimi a kasar nan, ba wai kawai za a kara yawan jami’oi ba. Bayan haka, ina ganin karin jami’oin zai taimaka wajen samar da aikin yi ga ’yan kasa, domin za a dauki malamai da sauran ma’aikata.”