✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko sabbin ministoci za su iya kawo canjin da ake bukata?

A makon jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci bikin rantsar da sabbin ministocin gwamnatinsa. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko sabbin…

A makon jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci bikin rantsar da sabbin ministocin gwamnatinsa. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko sabbin ministocin za su iya kawo canjin da ake ta hakilon gani a kasar nan ta fuskar inganta rayuwar al’umma? Wakilanmu sun gana da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Ministocin za su kawo canji – Rabi’u Tela

Muhammad Rabi’u Salisu Tela: “Ra’ayina game da batun ministoci kuwa shi ne, sababbin ministocin za su kawo canji nagari idan aka yi la’akari da yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya zabo nagari. Yaki da cin hanci da rashawa da Shugaba Buhari yake yi, ina da yakinin su ma ministocin za su yi koyi da shi don ganin an samu ci gaba mai ma’ana. Sannan tsawon lokacin da Buhari ya dauka kafin ya zakulo su kadai ya isa su yi duk abin da za su iya don ba mara da kunya.”

Sabbin ministoci alheri ne – Muhammad Zayyan

Ahmed Garba Mohammed, a Kaduna

Muhammad Zayyan Musa: “A ra’ayina game da wannan batu, zaben ministocin da aka yi kuma aka rantsar da su, ko shakka babu ina da yakinin za su kawo canji mai ma’ana. Na farko dai ka san aikin gwamnati, aiki ne na ci gaba don da ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ayyuka sun yi masa yawa, don haka a yanzu ya samu mataimaka a fannoni da dama.  Kuma yadda ake kuka da rashin kudi a fadin kasar nan, yanzu abubuwa za su yi sauki, ma’ana Buhari zai sakar wa ministocin kudi don su gudanar da ayyukan rasa kasa.  Ke nan zuwan ministocin alheri ne kuma zai kawo sauyi nagari in sha Allah.”

Ba tababa za su kawo canji – Khadija Ado

Abbas Ibrahim dalibi, a Legas

Hajiya Khadija Ado dansudu: “Tabbas ministocin za su kawo sauyin da zai yi tasiri a rayuwar ’yan Najeriya, kasancewarsu nagartattun mutane da Shugaba Buhari ya zakulo aka kuma tantance su, ya kuma ba su ma’aikatun da suka dace da su. Ina da tabbacin za su yi koyi da shi, su kawo mana kyawawan sauye-sauye.”

Za su kawo sauyi – Salisu Garba

Abbas Ibrahim dalibi,  a Abekuta

Alhaji Salisu Garba Bashankai: “E, ministocin Shugaba Muhammadu Buhari za su kawo sauyin da jama’ar kasar nan ke bukata, domin kuwa sai da aka tankade aka rairaye aka zabo ingantattun mutane sannan aka ba su ma’aikatun da suka dace da su. Hakazalika, za suyi koyi da Shugaba Buhari domin ya san iyawa da kwarewar wadanda ya zabo kuma idanun al’ummar kasar na kansu kacokan. Don haka wajibi ne su yi iya kokarinsu don kawo ingantaccen sauyi.”

Ministocin za su iya – Abbas Isma’ila

Ahmad Kabir, a Katsina

Alhaji Abbas Isma’ila: “Duk da mun san cewa Allah ne ke kawo sauyi a duk lokacin da Ya so da kuma inda Ya so, muna ganin lallai wadannan ministoci da Allah Ya nufi Shugaban kasa Buhari ya zabo mana; lallai za su yi nasara ta sauya abubuwa da dama da mu ’yan kasa muke bukata a yanzu. Mu dauki misalin ko wannan matsala da ta addabi kasar nan, ta Boko Haram, in aka dubi wadanda aka aza wa wannan nauyi, musamman shi Ministan Tsaro, in da Buhari ya san ba zai iya ba, babu yadda za a yi ya aza shi. Gaskiya muna da tabbacin za su ba mara da kunya, illa kawai mu rika yi masu addu’ar fatan alheri. Amma gaskiya yanzu ne aka samu wadanda za su fitar da Najeriya daga cikin irin mawuyacin halin da take ciki.”

Za su iya kawo canji – Anas Rabe

Ahmad Kabir, a Katsina

Anas Rabe Kafinta: “Sosai, wadannan ministoci za su iya kawo sauyin da ake bukata. Duk da halin da kasar take ciki amma suka yarda suka amshi wadannan mukamai, lallai za su yi iya kokarinsu na ganin cewa sun fidda shi Shugaban kasa daga kunya. Kazalika za su yi kokarin fitar da su kansu kunya saboda sun san irin kalubalen da ke gabansu. Har’ila yau, idan aka dubi kowane ofis da aka ba shi wannan minista, aka kuma tuna tarihinsa da irin ayyukan da ya yi ko yake yi, lallai an san zai yi bakin rai bakin fama; domin ganin cewa an kawo duk wani sauyin da jama’ar kasar nan ke bukata. Saboda haka muna da yakinin cewa wadannan ministoci za su kawo sauyi na alheri a kasar nan.”