✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko na samu aiki ba zan bar sana’ar lalle ba

Lalle na daga cikin abubuwan kwalliya da mata ke yayi a wannan zamanin bayan kwalliyar fuska da gyaran jiki iri-iri da suka zamo jiki kuma…

Lalle na daga cikin abubuwan kwalliya da mata ke yayi a wannan zamanin bayan kwalliyar fuska da gyaran jiki iri-iri da suka zamo jiki kuma na yayi.

Kowacce shekara ko juyi akan samu wani samfurin lalle da ake yayi tun daga kan amare har zuwa ’yan mata da matan aure da kananan yara domin kara wa hannuwansu da kafafunsu kyau, da kuma fito da kalarsu.

Bayan lalle na gargajiya da aka saba yi tun iyaye da kakanni, akwai baki da na kwali da ya shigo ya kuma samu gurin zama a gun matan, musamman saboda maza kan yaba da kyansa, wani lokacin ma har su kara da kyauta, bayan bada kudin biyan mai kunshin.

Haka kuma bayan kwalliya da ake yi da shi, matan kan dandashe jikinsu da shi a gyaran jiki musamman na amare, da turara shi a matsayin magani, da kuma amfani da bakinsa da ake kira da sibka wajen rina gashi ya koma baki, sannan a dora masa man gyara gashi na Relaxer.

Wannan ya sanya guraren gyaran gashi na zamani ba ka raba su da Sibka, yadda yake sanya gashi bakikkirin ya kuma kwanta bayan an busar da shi da na’ura (dryer).

Baya ga mata kuma, akwai maza da su ma ke amfani da shi wajen gyaran gemu, wanda kan sanya shi ya yi jawur musamman dattijai, kasancewar malamai na bayyana hakan a matsayin abin samun lada.

Wannan ya sanya muka tattauna da masu ruwa da tsaki a harkar lallen, kan yadda ake samarwa, sarrafawa, da amfani da shi, har ma da muhimmancinsa ga lafiyar dan Adam a mahangar addinin Musulunci da gargajiya da kuma likitance.

Lalle a Gona

Noman Lalle, Sarrafa Shi, amfaninsa da kasuwancinsa:

Malam Abdulmuminu Haruna manomi ne a Jihar Kano, ya kuma ce ba sa noman lalle shi kadai a gona, sai dai su yi kewaye da shi, duk da ribar da ake samu da noman sa.

“Kamar yadda kike gani, duk inda lalle yake a gonar nan, to iyaka ce ta gona, ba ma noma shi shi kadai, amma dai yanzu saboda muna samun riba muna kara yawansa a iyakar.”

“Hakan ne ya sa wasu ba su damu da sanya masa taki su yi masa cikakken noma ba, amma duk wanda ya kula da shi kamar yadda zai kula da sauran gonarsa, duk da a iya iyakar ya shuka, to ya fi cin riba”.

“Dalili kuwa shi ne kin ga har daga kasashen ketare yanzu ana zuwa neman lallen nan, saboda abu ne da duniya ke yayin sa, kuma su sun san me suke yi da shi bayan kwalliyar ma”, in ji Abdulmumin.

Sarrafa shi kafin kaiwa kasuwa

“Kin ga yanzu ba a yankar sa har sai ya shekara lokacin kaka ke nan.

“Idan ya shekara kuma aka fara yankar sa, shi ana yankar sa yana kara tofo da fadi ne.

“To wanda ka yanka za ka tara shi a gona ya bushe, sai ka sa sanda kana girgizawa kana karkadewa, sai a dura shi a buhu a dinke da basilla, a kai shi kasuwa.

“Kakar da ta wuce mun siyar da buhunsa N5,000, amma da ya wuce kaka har N10,000 mun siyar da shi, amma shekarun baya N1,000 zuwa N500 muke siyar da shi, kinga kullum yana kara daraja ne, saboda kamar yadda na fada miki, ana fitar da shi waje.”

Nau’ikan lalle

Busasshen ganyen lalle kafin a nika

Musa Gwamnati wani dan kasuwa ne da ke sayar da lalle a Kasuwar Kurmi da ke Kano, ya kuma bayyana mana cewa lallen ma kala-kala ne.

Daga ciki akwai dan Rimin Gado da dan Garun Malam da Dan Nijar, da Dan Sakkwato.

Sauran sun hada da Dan Kademi da Dan Gaya da na Hausa.

Dangane da bambamcin wadannan nau’ikan kuma, Musa Gwamnati ya ce kowanne da irin kamun da yake da shi, da kuma irin kayan hadin da ake sanya masa kafin ado da shi.

“Ana saka masa kayan hadi irin su Karkar da Muhallabiya da Nashad da gishirin kunshi da sauran su; Kowanne da wanda ya fi dacewa da daya daga cikin nau’ikan nan da na fada miki.”

Yadda ake sarrafa shi

Dangane da yadda ake sarrafa shi kafin a sayar da shi kuma, Gwamnati ya ce sukan fara daka shi ne, kana su kai inji a nika, kasancewar ba zai niku ba saboda yana da santsi idan yana tsabarsa, sai an lallasa shi.

Kasuwancinsa

“Kamfanoni sun fi zuwa saye, saboda suna hada shi a hada atamfofi kuma musamman da kaka an fi cinikinsa — yana sabo ke nan”

Sannan wadanda suke shigowa daga waje domin sayen sa maza ne, musamman daga kasashen Sanigal, da Ikwitoriyal Gini, har ma da Santiral Afirka.”

Haka kuma ya ce sana`a ce da ya ke matukar samun nasibi da har zai ba wa matasa shawara da su rike ta, don ita kadai ba tare da an hada ta da wata ba ta ishi mai iyali.

Garin Lalle a kasuwa

Muhimmancinsa a addini

Dokta Isa Lawan, wanda aka fi sani da Mai Fada Da Aljanar Simbika ta Goron Dutse kuma Shugaban Cibiyar ba da Magungunan Musulunci ta Aba Zarril Gifari ya ce ba wai ado da lalle kadai ke da falala ba, hatta shuka shi ma a gida ko a gona na korar iskokai daga wuri, da sanya albarka ga sauran shukoki da ke kewaye da shi.

“Babban aikin lalle na farko shi ne idan mutum ya shafa shi a jikinsa yana ba shi kariya a jikinsa, musamman daga shafar aljanu.

“Wannan na daga cikin dalilan da suka sanya Annabi (SAW) ya ce maza su shafa shi a gemu, domin gashi ne hanyar da shaidan ya fi bin jikin dan Adam.

“Ba kuma lalle har sai gashi ya yi jawur ba, a’a sanya shi ko yaya ne a wanke ya wadatar.

“Ga mata kuma yana kara wa fatarsu lafiya, ga kuma kyau da yake kara wa hannunsu da kuma kore shaidan, shi jan lalle ke nan na gargajiya,” in ji Mai Fada Da Aljanu

“Idan tana yawan yin lalle, yana hana shaidan rabar ta,  musamman tafin hannu da kafa, saboda hannu ya fi saurin daukar cuta, yayin da kafa kuma ta fi daukar zafi, shi ya sa idan ka taka garwashi kake jin sa har tsakiyar kanka.

“Haka zalika ana hayaki da shi don kore aljanu, kuma ga riba da yake da ita ga manominsa, kuma yana bin kofofin jini ya wanke shi tas.

“Haka kuma yana sa farin ciki, saboda kin san yawan bakin ciki alamar aljanu ce; to idan kina yawan yin lalle ba za ki dinga yawan damuwar ba gaira ba dalili ba,” in ji shi.

Dangane da ko na zamani ya fada cikin wannan falala, Dokta Isa ya ce waccan falala ta lallen gargajiya ce, ba shi da tabbas din na zamani, kasancewar ba shi da masaniya kan sinadaran da ake  hade-hadensa da su.

Lalle a likitance

Dokta Nuruddin Haladu likita ne a Asibitin Fata na Bela a Jihar Kano, ya kuma ce babu wata illa da a likitance da aka taba ganowa lallen gargajiya na da shi har yanzu, sai dai dan abin da ba a rasa ba a bangaren na zamani da ake sanyawa sinadarai.

“Illar da za a iya cewa lalle na da shi sai dai ga wasu da bai karbe su ba, kamar sinadarin Haidrojin da ake sakawa a bakin lalle, sainadari ne mai karfi, ko mu a nan asibiti wanke gyambo ko wani ciwo muke yi [da shi] saboda kashe kwayoyin cutarsa kafin mu yi masa komai.

“To wasu idan bai karbe su ba yana sanya musu kuraje masu ruwa, ko ma kaikayi na tsawon lokaci da kashe farce yayi ta radadi, wadannan duk muna kiran su ‘allergy’.

“To banda wannan ko na zamanin gaskiya babu wata matsala ko alfanu da za mu ce lalle na da shi,” in ji likitan.

Bambamcin kunshin gargajiya da na zamani

Inna Yarinya, wata dattijuwa ce da ke zaune a unguwar Rimin Kira a Karamar Hukumar Birni ta Jihar Kano, ta ce a baya tun kafin zuwan leda, suna amfani ne da zani wanda ake kasanki da addagiri da shi, sai ganyen tumfafiya ko chediya domin tare lallen a kafa.

“Idan aka kwaba lallen a kwano, sai a shimfida wani yanki na zanin (shi ake cewa kasanki), sai a sassaka kunshin.

“Idan kin saka sai ki saka ganyen nan ki lullube da shi, sannan ki saka daya yankin atamfar (addagiri ke nan) a daddaura a jikin ganyen.

“Idan da daddaure aka saka kwana ake yi da shi, idan kuma da safe aka saka, to wuni ake da shi ko a cire zuwa Azahar.

“Shi kuma na hannu zuba kwababben lallen ake a cikin zunguru sai kawai a zura hannu a ciki.”

Zunguru
Zunguru

Lallen zamani:

Wata matashiya mai sana’ar kunshin zamani, Maryam Muhammad Na Allah, ta ce yin kwabin jan kunshin na gargajiya ya sauya ba kamar da ba.

“A da kin ga tsuran lallen ake kwabawa, amma yanzu ana saka abubuwan da ke kara masa launi da sauri, saboda zaman nan na da ba a iya yin sa yanzu.

“Shi kansa bakin akwai na gida akwai na Indiya wanda ya fi sauri da saukin yi.”

“Na gida shi ne wanda ake dafa sinadarin Haidrojin din kafin a hada, shi kuma na Indiya da kayan hadinsa ya ke zuwa, amma akan kara masa Haidrojin din don ba ya isa”.

Ribar sana’ar kunshi

“Sana’ar kunshi na da riba sosai gaskiya, don kinga tun ina makaranta da kunshi na biya wa kaina da kannena kudin makaranta, da ma wasu hidimdimuun gidanmu.

“Kin ga musamman a ce har gida ka je ka yi wa mace, ka ma fi samun alheri gaskiya, balle da Sallah kuma ko lokutan biki ko suna”.

“Don haka ina kira ga mata musamman matasa da su riki sana’arsu ta kunshi da muhimmanci, don ni ko aiki na samu gaskiya ba zan daina kunshi ba saboda yadda nake samun rufin asiri da shi.”

HADIN BAKIN KUNSHIN INDIYA
Hadin bakin kunshin Indiya.

“Kuma kin ga hawa farashinsa yake yi yanzu, iya hannu kadai jan kunshi na kaiwa N300, hannu da kafa kuma N800 zuwa N1,000 ne, na amare kuma daga N1,00 ne zuwa N2,000″.

“Akwai na salatif, shi kuma daga N2,000 ya fara saboda ya fi cin lokaci, sai kuma baki N300 ne iya hannu, idan kuma za a hada maka duka yana kai wa N1,500 zuwa 2,000”, in ji ta.

“Kin ga gaba daya sai ka kashe bai fi N1,000 ba, amma sai ka yi na 5,000 ma ko fiye da shi.”