✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko kun san siyasa?

Yara Manyan gobe, yau zan bijiro muku da tambaya ne game da siyasa, musamman ma a daidai wannan lokaci da za a gudanar da zaben…

Yara Manyan gobe, yau zan bijiro muku da tambaya ne game da siyasa, musamman ma a daidai wannan lokaci da za a gudanar da zaben shekara ta 2015. Ko kun san yadda ake yin siyasa?
Ni dai na san ba ku san siyasa ba, amma kun ga ana yi, tunda kuna ganin hotunan ’yan takara da tambarin jam’iyyu. Siyasa dai hanya ce ta samar da shugabanni nagari, masu manufa ta gari, don kyautata rayuwar al’umma.
Mutane masu ra’ayi da manufa ke kafa jam’iyyun siyasa. Sannan akwai Hukumar zabe ta kasa (INEC) da aka dora wa alhakin yi wa jam’iyyu rajista, tare da ’yan takara da wadanda shekarunsu suka kai na yin zabe.
Lallai ya kamata ku tambayi malamai da iyaye da kakanni, don su bayyana muku yadda ake gudanar da harkokin siyasa a kasar nan, domin ita ce hanyar da ake zabo shugabanni daga matakin kananan hukumomi zuwa kasa, wato daga kansila da Shugaban karamar hukuma zuwa kan shugaban kasa.
A matsayinku na Manyan gobe, za a samu wadanda za su yi siyasa a cikinku. To, tunda muna fatan ku zama manya nagari, wadanda za su iya warware matsalolin da ke damun al’umma, dole ne ku kara kwazo wajen karatu, ta yadda za kusan makamar aiki.
Don haka, wanda duk yake son zama shugaba nagari a cikin al’umma, ya zama dole yasan tarihin kasarsa da shugabanninta da al’adun mutanenta. Uwa-uba akwai bukatar mutum ya samu kwarewa a fannonin ilimi, wadanda suka hada da kimiyya da fasaha da kere-kere da nazarin tattalin arziki da makamantansu.
Manyan gobe sai a kara kwazo wajen karatu, a ci jarabawa, don tafiya makarantu na gaba, ta yadda al’umma za ta yi alfahari da ku  a matsayin shugabannin siyasa nagari. Wanda kuwa ya ki mayar da hankali wajen karatu, in bai yi sa’a ba, sai ya kare a bangar siyasa. Kowa yasan ’yan bangar siyasa ke tayar da rikici, don biyan bukatar wasu, shi kuma an yi amfani da shi, a karshe a yasar da shi. Wannan ya yi daidai da karin maganar Hausawa, cewa, “anci moriyar ganga, an yada kwaurenta.’
 Ku sani karatu da rubutu ko kwarewa a fannonin ilimi ke samar wa al’umma shugabanni masu tausayin al’umma, wadanda a kullum manufarsu kowa ya samu ilimi; a kula lafiyar al’umma, a bunkasa tattalin arziki, ta hanyar noma da kiwo da hakar ma’adinai, ta yadda zamantakewa za ta yi wa kowa dadi.