✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko harkar noma za ta dore a Najeriya?

Najeriya dai kasa ce da ke da burin ko bukatar ta wadata al’umarta da abinci. Kuma wannan ya sanya gwamnatoci da dama, kama daga na…

Najeriya dai kasa ce da ke da burin ko bukatar ta wadata al’umarta da abinci. Kuma wannan ya sanya gwamnatoci da dama, kama daga na sojoji zuwa na siyasa sun fito da shirye-shirye iri  daban-daban da nufin inganta harkar noma, amma har yanzu shiru kake ji hakar ba ta cimma ruwa ba. Ko harkar noma za ta dore a Najeriya? A baya, masana na ganin cewa, yawan fito da shirye-shirye da gwamnatocin kasar ke yi shi ke kawo cikas ga cimma wannan buri, sakamakon rashin dorewar shiri, al’amarin da masana ke dangantawa da dabi’ar wasu shugabanni ta son a ce gwamnatinsu ce ta fito da shirin da ya yi tasiri.

Kamar yadda ake yi wa sana’ar noma kirari da ‘na duke tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar,’ haka za a iya cewa sana’ar noma dadaddiyar sana’a ce a Najeriya, sana’ar da alkaluma suka nuna sama da kashi 70 cikin 100 na al’ummar kasar suka dogara da ita wajen samun biyan bukatun rayuwarsu. Haka zalika da noman ne Najeriya ta dogara wajen samun kudin shigarta kafin ta gano albarkatun mai. Sai dai tun lokacin da Najeriya ta fara cin gajiyar man fetur ne sana’ar noma ta koma ’yar bora. Kodayake wasu gwamnatoci da dama sun yi yunkurin bunkasa harkar noma ta hanyar fito da shirye-shirye da aka yi musu lakabi da Ingilishi, irin su “Operation Feed the Nation da Green Rebolution  da Back to Land,” da sauransu da kuma wasu hukumomi masu yawa da aka kafa da sunan bunkasa harkar noma.
A Najeriya dai kusan zai yi wuya a kafa wata gwamnati ba tare da ta fito da nata shirin na inganta harkar noma ba, inda wani lokaci akan zabi wani nau’in abinci, irin su shinkafa ko alkama ko rogo ko wani rukunin manoma da nufin ba su fifiko, inda ake kashe dubban miliyoyin Naira da sunan za a samu sauyi mai amfani a wannan lokaci, har a kai ga cimma burin wadata kasa da abinci kamar yadda wasu kasashen duniya suka yi nasara.
A zamanin gwamnatin Jonathan kasar nan ta bayyana kanta a matsayin kasa mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar Afrika, hasali ma Najeriya ita ce tafi kowace kasa a Nahiyar Afirka yawan man fetur, to sai dai abin da mutane da dama ba su gane ba, shi ne, irin gudunmawar da noma ya bayar a kasar kuma yake bayarwa wajen bunkasa tattalin arziki da kuma inganta halin rayuwar dimbin jama’ar Najeriya, musamman mazauna karkara. Najeriya na bukatar kara yawan kudin da ake kashewa a fannin noma fiye da kashi 1.7 cikin 100 na kasafin kudinta a halin yanzu. Tuni fannin noma ya fara nuna alamun cewa,  nan gaba zai iya farfado da tattalin arzikin Najeriya da na sauran kasashen Afirka. Muhimman manufofin da za a yi la’akari da su, su ne, wajen cimma wannan buri, na farko a samar da abin yi ga masu zaman banza, tare da fito da wasu hanyoyi don kaiwa ga kasuwanni cikin sauki, samar da inshorar kayan gona da aka noma, sannan sai shirin samar da tallafi kan takin zamani, wanda babu hannun gwamnati  wajen gudanarwa kana kuma da kara haraji kan kayan gonar da ake shigowa da su daga waje don kaiwa ga dogaro da kai.
Manoman dai suna ta kara kira ga wannan sabuwar gwamnatin karkashin Shugaba  Muhammadu Buhari da sauran gwamnonin kasar nan baki daya cewa su rika raba taki a kan lokaci ta yadda takin zai kai ga manoma. Idan muka dawo noman shinkafa da alkama a Najeriya samun sauye-sauye da dama, a yayin da gwamnati ta fara rage yawan garin alkama da ake shigowa daga waje, tana maye gurbinta da ingantaccen garin Rogo da ake burodi da shi. Ana kuma rage yawan sukarin da ake shigowa daga waje, saboda ana kara himmatuwa wajen sarrafa rogo, ta yadda ake samun irin amfani da shi wajen kara zakin abubuwa.
Mafita game da harkar noma a Najeriya ita ce dole gwamnati ta kara yawan tallafin da take bayarwa ga noma kamar bashi ta hannun bankin manoma haka kuma ta tabbatar manoman asali ne suke cin gajiyar wannan bashi sannan ta hana shigo da wasu daga cikin kayan abinci daga ketare, tallafawa da kuma saukaka dokokin fitar da kaya zuwa ketare, tallafa wa masana’antun noma da kiwo, ginawa da gyara hanyoyin yankunan karkara da ilimantar da manoma kan sababbin dabarun noma da kiwo na zamani da sauransu. Shi ma wannan ba karamin mafita ba ce ga al’umma musamman ta bangaren samun abin yi ga matasan karkara da birane. Kuma za a samu raguwar yaduwar ta’addanci a kasa. Duk da dai wannan gwamnati ta dan fara samun ci gaba musamman a sababbin tsare-tsare da Ma’aikatar Gona ta Tarayya ta bullo da su, amma muna fatan hakan zai dore don a yaki yunwa da fatara.
Ja’en, shi ne Sakataren Kudi na kungiyar Muryar Talaka, Reshen Jihar Kano.
Imel: [email protected]
07033882307.